China zata taimakawa Nigeria a fannin tsaro

0
19

Gwamnatocin Najeriya da China sun amince su ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin makamashi, da tsaro, da harkokin kuɗi.

Ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu ne suka bayyana hakan a yau Alhamis, sakamakon ziyarar da ministan harkokin wajen China, ya kawo Nigeria

Ministan Harkokin Wajen China Wang Yi na ziyara a Najeriya ne a wani ɓangare na ziyarar aiki a ƙasashen Afirka huɗu domin faɗaɗa tasirin China, a nahiyar.

Wang, ya ce China za ta duba buƙatar da Najeriya ta gabatar mata ta faɗaɗa yarjejniyar amfani da takardun kuɗin ƙasar na Yan.

A ɓangaren tsaro kuma, Wang ya ce China za ta dinga goya wa Afirka baya koda yaushe a zauren tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here