Shin kun tuna da cewa shugaban Nigeria Bola Tinubu, yayi alkawarin bayar da damar shigowa da kayan abinci cikin Nigeria daga ketare ba tare da haraji ba ?
Sai dai har yanzu babu wani dalili da gwamnatin ta sanar a matsayin abin da ya hana aiwatar da hakan.
A yanzu fiye da kwanaki 180 kenan aka kwashe da yin alkawarin, na cewa za’a bawa yan kasuwa damar shigo da kayan abinci, ba tare da karbar haraji ba, don saukakawa al’umma kuncin rayuwa da yunwa da ake ciki.
A baya shugaban hukumar hana fasa kwauri shima ya tabbatar da cewa zuwa wani dan lokaci za’a bude hanya ga masu son shigo da kayan abinci da gwamnatin tace za’a iya shigo da su.
Abin tambayar a nan shine gwamnatin tarayya ta manta ana fama da wannan tsadar rayuwa da kayan abinci ne, ko kuma masu samar da kayan abinci a cikin gida ne ke yiwa manufar kafar ungulu don kar kayan abinci yayi sauki.
A bangare guda kuwa wasu suna ganin cewa gwamnatin Tinubu, bata mayar da hankali wajen cika alkawarin saukakawa mutane, kamar yadda aka gani lokacin da kamfanin NNPCL yace zai rage farashin litar man zuwa 935.