Jami’an yan sanda sun samu nasarar kama wasu direbobin manyan motoci su biyar da suka sace buhu 1,840 na abincin tallafin da Majalisar ĆŠinkin Duniya, ta bayar a Najeriya.
An kama direbobin a hanyar su ta yin safarar kayan abincin na buhunan alkama da suka sace zuwa Jihar Kano daga tashar jiragen ruwa ta Fatakwal da ke Jihar Ribas.
Ana zargin direbobin sun sace buhunan abincin tallafin shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) kamar yadda Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ribas, Jimoh Moshood, ya sanar.
Kwamishinan ya ce ana neman wasu direbobi biyu da wasu mutane da suka tsere kan satar abincin tallafin.
Kwamishinan yace akwai buhu fiye da 600, na alkama wanda aka nema aka rasa.
Ya ce an kwace motoci biyu da aka yi amfani da su wajen aikata satar sannan kotu ta É—aure masu laifin.
Zuwa yanzu an samu nasarar mikawa ofishin WFP, na majalisar Dinkin Duniya, buhu 1,238, na abincin da aka kwato, sannan ana binciken ragowar.