Gwamnan Akwa Ibom ya kori baki dayan kwamishinonin sa

0
11

Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya rushe baki dayan majalisa zartarwar sa, inda yace a yanzu haka yana bukatar nada sabbin mutane a mukaman wadanda ya kora.

Umo Eno, ya sanar da hakan a yau juma’a, lokacin gudanar da wani taro, yana mai cewa babu daya daga cikin kwamishinonin sa da bai yi kokari a aikin da aka bashi ba.

Gwamnan yace daukacin kwamishinonin nasa sun yi kokarin sauke nauyin aikin da aka dora musu, yana mai jaddada cewa an sauke su ne saboda a bawa wasu mutanen damar nuna irin tasu basirar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here