Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta nemi a ware mata naira biliyan 126, a cikin kasafin kuÉ—in shekarar 2025, da muke ciki don gudanar da ayyukan ta.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana haka ranar Juma’a, data gabata a lokacin da yake kare kasafin kudin hukumar a gaban kwamitin majalisun dokokin Æ™asa mai kula da kasafi don kare kasafin kuÉ—in hukumar.
Yakubu, ya nuna kin amincewa da naira biliyan 40, da aka ayyana a matsayin kudin da INEC zata kashe tun da farko, a matsayin kasafin ta, inda yace a yanzu an samu tsadar rayuwa, wanda suma kayan ayyukan hukumar sun samu karin farashi.
Farfesa Yakubu, yace lamarin zabe abu ne mai bukatar kudade da yawa, inda yace suna da hujjar yadda zasu yi amfani da kudaden.
Daga cikin ayyukan da ya ce hukumar za ta gudanar a shekarar 2025 sun haɗa da cigaba da aikin rajistar masu zaɓe, da shirya zaɓukan wasu jihohin a bana, da sauya wasu kayyakin zaɓen da suka lalace da gyara ofisoshin hukumar da ke wasu jihohin Nigeria.
Ya kuma ce shekarar 2025, shekara ce mai muhimmanci ga hukumar wajen shiryawa gudanar da zaɓukan 2027.