Kamfanin NNPCL ya karkatar da naira triliyan 2.68

0
8

A daidai lokacin da matsalolin kudi suka dabaibaye Nigeria, Kuma hakan ya kawo mummunan tasiri ga yanayin tattalin arziki, babban mai binciken kudi na gwamnatin tarayya, ya zargi kamfanin mai na NNPCL, da karkatar da kudaden da yawan su yakai dala miliyan 19.77, kwatankwacin naira triliyan 2.68, a cikin shekara hudu, da suka wuce.

Wani binciken jaridar Punch, da aka fitar a yau lahadi, ya nuna cewa rahoton mai binciken kudi na gwamnatin tarayya da ake fitarwa Shekara bayan shekara, ya nuna cewa a tsakanin shekarun 2017-2021, an karkatar da naira triliyan 1.33, a 2017, sai naira biliyan 681.02, a 2019, da naira biliyan 151.12, a 2020, sai kuma naira biliyan 514, a 2021.

Bisa lissafi a wadannan Shekaru an sace kudaden da yawan su yakai dala miliyan 19.77, a kamfanin NNPCL.

Rahoton karkatar da kudaden wanda aka mikawa majalisun dokokin kasa, ya nuna cewa an Karya dokokin harkokin kudi, na Nigeria da aka samar a shekarar 2009.

Punch, tace wakilin ta ya gano cewa kamfanin NNPCL, bai ce uffan dangane da batun zargin sa da kwashe kudaden ba, daga babban mai binciken kudi na kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here