Gwamnatin Nigeria tace zuwa yanzu ta kammala yanke hukuncin bawa kamfanonin jiragen sama 4, damar yin jigilar maniyyatan kasar zuwa kasa mai tsarki don sauke faralin shekarar 2025.
Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta kasa NAHCON, Farfesa Muhammad Usman, ne ya sanar da hakan a jiya lahadi, yana mai cewa tun da farko kafanonin jiragen sama 11, ne suka nuna sha’awar su ta yin jigilar kafin a kammala yanke hukuncin wadanda za’a zaba.
:::Sojojin Nigeria sun kai harin kuskure kan fararen hula sau 11
Ya ce kamfanonin sun hadar da Air Peace, Fly-Nas, na kasar Saudiyya da Max Air, sai kuma UMZA Aviation.