Nigeria zata toshe hanyoyin da Boko Haram ke samun kudade daga ketare

0
11

Hafsan Hafsohin kasa Christopher Musa, yace kungiyar Boko Haram, tana samun tallafin kudade daga ciki da wajen Nigeria, wanda haka ne yasa har yanzu kungiyar ke matsayin wata babbar barazana duk da kokarin da ake yi na kawar da ita.

Idan ba’a manta ba, an fara samun rikicin Boko Haram a Nigeria, tun a shekarar 2009, wanda ta samo asali daga jihar Borno, ta gabashin kasar nan.

:::Eric Chelle ya zama cikakken mai horas da Super Eagles

Tun daga wancan lokaci gwamnatoci ke cewa suna yin bakin kokari wajen yakar ayyukan kungiyar da ya zama sanadiyyar mutuwar dubban mutanen da ba’a san adadi ba, tare da raba miliyoyi da mahallin su.

Musa, ya sanar da hakan a yayin da ake zantawa dashi a talbijin ta Arise, a yau litinin, inda ya tabbatar da cewa yan ta’addan kasar nan, suna samun tallafin kudi daga ketare.

Yace daga cikin matakan da suke dauka akwai yin aiki da ofishin mai bawa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, da babban bankin kasa, DSS, da hukumar leken asiri ta kasa, don rufe hanyoyin da kungiyar yan ta’addan ke samun tallafin kudi.

Hafsan Hafsoshin kasar, yace suna sane da hanyoyin yin garkuwa da yan ta’adda ke samun kudade dasu, kuma zasu takawa hakan birki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here