Ssojojin Nigeria sun kai harin kuskure kan fararen hula har sau 11, wanda hakan ke yin sanadiyyar mutuwar mutanen da basu ji ba basu gani ba, ta hanyar bama-baman, da sojoji ke sakar musu daga sama.
A mafi yawancin lokaci sojojin suna cewa harin yana faruwa lokacin da suke yunkurin farmakar yan ta’addan arewacin kasar.
Sai dai wasu mutanen na danganta hakan da rashin sanin makamar aiki, ko kuma yin hakan da gangan, bisa hujjar cewa ya kamata zuwa yanzu a kawo karshen kisan mutane da jiragen sojojin saboda an fuskanci hakan ba sau daya ko biyu ba.
Jihohin Borno, Kaduna, da Sokoto, na daga cikin yankunan da suka fi samun asarar rayukan mutane saboda harin sojoji kan yan ta’adda.
Babban dalilin dake kawo hakan baya rasa nasaba da yanda yan ta’adda ke buya a unguwannin da mutane yan babu ruwa na suke yin rayuwa ba, da wani sa’in ake samun tsautsayin kai musu hari lokacin da ake kokarin kashe yan ta’addan.
Hare haren da aka kai zuwa kan yan babu ruwa na sun hadar da;
1.Harin Nachade dake Jamhuriyyar Nijar, wanda sojojin suka yi kuskuren kashe mutane a ranar 20 Fabrairun 2022
2. Sai harin Kunkuman Bayan Dutse jihar Katsina, na ranar 7 Yulin 2022
3.Mutumji – Jihar Zamfara, a ranar 19 Disamba 2022
4.Mainok – Jihar Borno, a ranar 25 Afirilun 2021
5.Kwatar Daban Masara – Jihar Borno, a ranar 28 Satumba 2021
6.Doma – jihar Nasarawa, a ranar 27 Janairu 2023
7.Rann – jihar Borno, a ranar 18 Janairu 2017
8.Buhari – jihar Yobe, a ranar 15 Satumba 2021
9.Tudun Biri – Jihar Kaduna, a ranar 3 Disamba 2023
10.Silame – Jihar Sokoto, a ranar 25 Disamba 2024
11. Hari na karshe shine wanda aka kai kauyen Tungar Kara a Jihar Zamfara, cikin ranar 11 Janairu 2024
Baki dayan wadannan wurare sun fuskanci harin kuskure daga sojojin Nigeria, da hakan ya kawo mutuwar mutane masu yawan gaske.