Yan ta’adda sun kashe masu ibada a Cocin Chibok

0
36
Borno
Borno

Wasu da ake zaton yan ta’adda ne sun kashe mutane biyu masu zuwa yin ibada a cocin Ekklesiyar Yanu’wa, dake karamar hukumar Chibok, a jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Borno, ASP Nahu Daso, ya tabbatar da labarin harin ga wakilin jaridar Punch, a Maiduguri, yana mai cewa, jami’an su sun bazu tare da sanya idanu don gano masu hannu a aikata laifin, tare da kwantar da hankalin al’ummar yankin da abin ya faru.

:::Bama kai hari da niyyar kashe fararen hula—Sojin Nigeria

Yace bayan faruwar harin babban ofishin yan sanda na Chibok, ya sanar da su cewa wasu mahara sun zo tare da yin harbin kan mai uwa da wabi, wanda akayi rashin sa’a hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutum biyu.

An kai harin da karfe 2, na daren ranar lahadi, lokacin da mutanen ke yin bauta, bayan haka kuma maharan sun kone shaguna 7, don jefa firgichi ga al’umma, kamar yadda mutanen yankin da abin ya faru suka sanar.

Nahum, ya kara da cewa bayan wadanda suka mutu akwai wasu mutane 2 da suka ji munanan raunika.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here