Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo ya bayyana cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu, tayi a matsayin wani alheri kai tsaye ga gwamnatocin jihohi.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake duba wasu ayyuka na murnar cika shekara ta farko a wa’adinsa na biyu.
Ya ce yanzu haka akwai karin kudade da ke shiga asusun gwamnatocin jihohi domin yin ayyukan cigaba daga tarayya.
:::Amurka tace za’a tsagaita wuta a yakin da Isra’ila ke yi da Falasdinawa
Yace yana ganin idan aka kwatanta munanan illolin cire tallafin man fetur da kuma fa’idojin da suka shafi zamantakewa da ababen more rayuwa, da fa’idar zamantakewa, da saukin yin kasuwanci da aka samu ta hanyar samar da ababen more rayuwa, cire tallafin alheri ne.
Uzodinma, ya kara da cewa cire tallafin man fetur abin alheri ne ga yan kasa, ba wai abin cutarwa ba, domin yanzu sun samu karin kudade a jihohi, kuma dole ne gwamnatocin jihohi su yi wani abu don nuna wa ‘yan kasa cewa za su iya samar da abubuwan cigaba domin a yanzu sun samun karin kudade, sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
Uzodimma dai ba shi ne gwamna na farko da ya yi irin wannan ikirarin ba, ko a shekarar da ta gabata Gwamna Abdullahi Sule, na Jihar Nasarawa, ya bukaci ‘yan Najeriya, su binciki gwamnatocin jihohin su kan yadda suke tafiyar da abin da suke samu daga gwamnatin tarayya, saboda an samu karin kudin da gwamnoni ke karba daga tarayya.
A lokacin gwamna Sule, yace yan kasa suna shan wahala duk da cewa gwamnatin tarayya tana bawa jihohi kudaden daya kamata ace mutane sun samu saukin kuncin da suke ciki.