Farashin fetur ya tashi a Defo-Defo

0
68
man fetur
man fetur

Akwai yiwuwar farashin litar man fetur zata yi tsada, zuwa karin kaso 4.74, akan kuÉ—in kowacce litar, biyo bayan yadda aka samu tashin farashin a defo defo.

Karin farashin yazo sakamakon tashin farashin danyen man a kasuwar duniya daga Dala 73 zuwa Dala 80, akan kowacce ganga.

Tuni wasu defo-defo, suka kara farashin ga masu gidajen mai dake saro man.

Daga cikin dafo din akwai wanda suka kara farashin daga naira 907, zuwa 950, duk lita daya.

Sahara defo, suma sun kara farashin daga naira 910, zuwa 950, sai defo din Shellplux daga naira 908 zuwa 960.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here