Wasu mutanen jihar Kano su 19 mahalarta ɗaurin aure a jihar Filato, sun gamu da ajalin su a hanya inda motar su ta kama da wuta sannan ta kone kurmus, a karamar hukumar Pankshin.
Daga cikin wadanda hatsarin ya rutsa dasu akwai mutane 11, da suka tsira da rayuwar su, a hanyar dawowa daga auren da aka daura ranar asabar data gabata a karamar hukumar Barkin Ladi.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Pankshin, John Dasar, yace mutanen sun mutu sakamakon motar su ta kama da wuta, sai dai an yi nasarar ceto direban motar da wasu fasinjoji.
Ya ce, an ceto mutane 11 amma mutane 19 sun kone ƙurmus ba za a iya gane su ba, saboda bayan mutane sun zo ana ƙoƙarin ceto fasinjojin ne motar ta kama da wuta, ta cinye ragowar.
Ya ce an kai waɗanda suka tsira da raunuka zuwa babban aibitin Pankshin don duba lafiyarsu.