Guguwa mai karfin gaske, na barazanar haifar da ƙarin gobara a sabbin wurare da dama na birnin Los Angeles, bayan shafe mako guda jami’an kashe gobara na ƙoƙarin kashe wutar da yanzu haka ke cigaba da fantsama yankunan da babu ita.
:::Gwamnan Zamfara ya gana da masu binciken harin sojoji daya kashe fararen hula
Masana harkokin hasashe sun ce wani mummunan abu ka’iya faruwa a yau laraba, saboda tasirin yanda wutar ke ci babu tsayawa.
Hukumar hasashen yanayi ta ƙasar Amurka, ta ce guguwar na iya mayar da hannun agogo baya, kan nasarar da aka samu ta cin ƙarfin wutar a wasu gurare.
An yi ƙiyasin cewa gobarar wadda ta faro daga daji ta janyo asarar da ta kai dala biliyan ɗari biyu da saba’in da biyar, sannan ta shafe sama da mako guda tana ci ba tare da an iya kashe ta ba, inda ta lalata dubban gidaje da kashe aƙalla mutum 25.