Mayakan kungiyar yan ta’addan Boko Haram, sun kai wani sabon hari jihar Borno, inda suka kone wata majami’a da gidajen mutane a garin Shikarkir, a karamar hukumar Chibok.
:::Ana tsoron gobarar Amurka zata kai inda ba’a zato
Mayakan sun kai wannan farmaki kwana guda bayan da suka kai makamancin sa a yankin Bazir, da shi kuma suka hallaka mutane 2, da kone wata Coci.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da kai harin Bazir, amma ya ce ba shi da labari akan harin Shikarkir.
Wani wanda aka ƙona masa gida mai suna Daniel Shikarkir, ya tabbatar da kai harin, inda yace kafin a kai musu harin yan Boko Haram din sun kai makamancin harin a wasu yankunan dake makwabtaka da su.