Hukumar kula da lantarki ta ƙasa, ta ce ta fara yin nazari akan miƙa ragamar kula da harkokin wutar lantarki ga jihohi.
Idan haka ya tabbata matakin zai bawa jihohi damar sa ido da tsawatarwa kan yadda ake tafiyar da harkokin samarwa da raba wutar lantarki a cikin su.
Daukar matakin ya samo asali bayan samar dokar gudanar da ayyukan wutar lantarki wadda ta bai wa jihohin kasar nan karfin iko kan harkokin samarwa da rarraba wutar.
:::CBN ya ci bankuna 9 tarar naira biliyan 1.35, saboda kin saka kudi a ATM lokacin Kirsimeti
Matakin zai taimakawa gwamnatin tarayya ta samu saukin saka ido da tafiyar da sha’anin wutar da a yanzu ke yawan samun matsala, musamman ma babban turken lantarkin dake kawo wuta arewa.
Ko a litinin data gabata sai da ministan lantarki ya bayyanawa majalisar dattawa cewa za’a cigaba da fuskantar lalacewar babban layin wutar, saboda gwamnati bata kammala gyaran wanda ya lalace sanadiyyar ayyukan yan ta’adda ba.