Wasu manoma 7, maza 2, mata 5, sun rasa rayuwar su bayan da wani hatsarin mota ya rutsa dasu a hanyar Kutigi-Batati zuwa Mokwa a karamar hukumar Lavun ta jihar Niger.
:::Boko Haram sun kone Coci da gidajen mutane a Borno
Daily Trust, ta rawaito cewa hatsarin ya faru lokacin da wata mota kirar Toyota, tayi karo da wata babbar motar tirela a kauyen Panti.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa direban mota Toyota, ne yayi sanadiyyar afkuwar hatsarin lokacin da yayi niyyar aron hannu don wuce babbar motar dake gaban sa.
An ce motar Toyotar, ta taho ne daga Batati, inda zasu je Kutigi, ta karamar hukumar Lavun, yayin da ita kuma babbar motar ta taso daga Lagos don zuwa Abuja.
Shugaban hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC, reshen jihar Niger, Kumar Tsukwam, ya tabbatar da afkuwar hatsarin, wanda yace ya faru tun a ranar litinin data gabata da misalin karfe 6, na yamma.