Hukumar kididdiga ta kasa NBS, tace tashin farashin kayayyakin masarufi ya karu zuwa kaso 34.80, a watan Disamban shekarar 2024.
A watan Nuwamba dai hauhawar farashin ta tsaya akan kaso 33.60.
Hukumar NBS, ta sanar da hakan a yau laraba, cikin rahoton da take fitarwa daya shafi farashin kayayyaki a Nigeria.