Majalisun dokokin kasa sun kara yawan kudin shigar da hukumar hana fasa kwauri, ta kasa Custom, zata tattarawa gwamnatin tarayya daga naira triliyan 6.5, zuwa triliyan 12, a wannan shekara ta 2025.
Shugaban kwamitin kudi na majalisar dattawa Sani Musa, da takwaransa na majalisar wakilai James Faleke, ne suka kara adadin kudin shigar da hukumar Custom, zata tattara, a ranar talata, lokacin da shugaban hukumar Adewale Adeniyi, ke kare kasafin kudin ma’aikatar sa na 2025.
Adeniyi, yace zasu iya tattara naira triliyan 6.5, sakamakon sun tattara triliyan 6.1, a shekarar 2024.
Sai dai majalisar ta mayar masa da martanin cewa kasafin kudin wannan shekara ya wuce ace naira triliyan 6.5, hukumar hana fasa kwaurin zata tattara.