Wata kotun tarayya a Legas dake Najeriya ta bada umarnin kwace wasu kadarori 14 mallakar gwamnatin jihar Kogi a biranen Abuja da Lagos da kuma kasar Daular Larabawa.
Sanarwar da mai magana da yawun Hukumar EFCC, dake yaki da almundahana, Wilson Uwujaren tace umarnin na wucin gadi ne har zuwa lokacin da za’a kammala shari’ar da suka gabatar na zargin rub da ciki da kudaden talakawa da kuma halarta kudaden haramun.
Uwujaren ya bayyana cewar alkalin kotun Nicholas Oweibo ya kuma bada umurnin killace naira miliyan 400 da aka samu hannu wani da ake kira Aminu Falala.
Hukumar tace an kwace kudin ne saboda zargin cewar an samo su ne ta haramtattun hanyoyi domin sayen wani fili mai lamba 1224 a layin Bishop Oluwole dake unguwar Victoria Island a birnin Lagos.
Idan ba’a manta ba Hukumar EFCC ta gurfanar da wani ‘dan uwan gwamnan Kogi Yahya Bello wanda ake kira Ali Bello a ranar 8 ga watan nan tare da Abba Adauda da Yakubu Siyaka Adabenege da Iyada Sadat saboda zargin halarta kudaden haramun da kuma batar da kudin da ya kai sama da naira biliyan 3.
Rahotanni sun ce uwargidan gwamnan Rashida Bello da ake zargin tana da hannu a badakalar tayi batan dabo.
ALLAH YAKYAUTA