Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fara rabon kayan zabe a fadin kasar baki daya domin gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi ranar asabar.
Kayayyakin da aka raba sun hada da na’urar tantance masu kada kuri’a (BVAS) da takardar sakamakon zabe da kuma takardar zabe daga babban bankin Najeriya (CBN).
Rabon wanda har yanzu ake ci gaba da yi a fadin kasar, ya samu halartan dukkanin hukumomin tsaro da suka hada da jami’an tsaro; ‘Yan sanda, Sojoji, da wakilan jam’iyyun siyasa da ke cikin zaben.
Hukumomin tsaro sun yi alkawarin yin adalci da kwarewa wajen gudanar da ayyukansu na zabe.
A baya an ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ta haramtawa jami’anta da sauran jami’an tsaro da ke da alaka da gwamnoni, ministoci da sauran jami’an gwamnati rakiya zuwa rumfunan zabe a zaben 2023.
Wannan shi ne kamar yadda ta ba da umarnin hana zirga-zirga a kashi na farko na babban zaben 2023 – na Shugaban kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa.
Hedikwatar rundunar, a daren Laraba, ta sanar da cewa, Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya bayar da umarnin hana zirga-zirga a kan tituna, magudanar ruwa, da sauran hanyoyin sufuri, daga karfe 12 na safe zuwa 6 na yamma a ranar zabe.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, CSP Muyiwa Adejobi ya fitar, ta ce wadanda ke gudanar da ayyuka masu muhimmanci kamar hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, jami’ai, masu sa ido, motocin daukar marasa lafiya, ‘yan kwana-kwana da dai sauransu, an kebe su.
Kakakin ya bayyana cewa, umarnin wani bangare ne na matakan da aka dauka don tabbatar da tsaro, da muhalli mai kyau don gudanar da zaben.