Yadda jami’an EFCC suka yi dirar mikiya a rumfunan zabe a Zamfara

0
95

Jami’an Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) sun yi dirar mikiya a wasu daga cikin runfunan zabe a jihar Zamfara yayin da ake tsaka da gudanar da zabe a ranar Asabar din data gabata.

Wuraren da suka kai sumamen sun hada da Akwatu mai lamba 025 Kanwuri Bugabuga da ke karamar hukumar Maradun da rumfar zabe ta mazabar gwamna Bello Matawale da ke cikin maradun da kuma rumfar dan takarar gwamna a Jamiyyar PDP na Jihar Zamfara, Dokta Dauda Lawal Dare, wato Women Center a Akwatu mai Lamba 012,a mazabar Madawaki cikin karamar hukumar Gusau.

Bayyanar EFCC a rumfunan zabe ya sanya wa ‘Yan siyasa karatun ta nutso kuma ya kawo gudanar da zaben cikin lumana da kwanciyar hankali.

Duk da tsaiko da aka samu na rashin kai kayan zaben a wasu mazabun Kananan hukumomin Tsafe da Gusau amma Jama’a sun yi dafifi a rumfunan zaben na su tun misalin karfe 8 na safe har zuwa daya da rabi na rana suna jiran kayan zaben don zabar wanda suke ra’ayi ba tare da hayaniya ba.

Kazalika duk da Jamiyyun a jiya suna ta hikamr bayar da kayan abinci da Atamfofi ga mata don su zabe su idan sun zo kada Kuri’a daga bisani sun yi batan dabo a mazabunsu dan gudun yin kicibus da Jami’an EFCC.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahotan LEADERSHIP HAUSA bata samu labarin kama wani da EFCC ta cafke ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here