Atiku ya bukaci INEC ta umarci jami’anta da su shigar da sakamakon zaben su a yanar gizo

0
114

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bukaci shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, da ya umurci jami’an tattara sakamakon zabe da su tura sakamakon zabe a manhajar INEC ta yanar gizo da gaggawa.

Atiku, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce kiran ya zama dole sabida a dakile yunkurin wasu gwamnoni da ke kokarin yin magudin zabe a wuraren tattara sakamakon zabe na kananan hukumomi.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankulan su, amma su lura su tabbatar da cewa masu adawa da dimokuradiyya ba su sace ‘yan cinsu ba ta hanyar lalata akwatunan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here