Atiku ya kayar da Tinubu a Kaduna

0
90

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya lashe zabe a Jihar Kaduna.

Atiku ya lashe zaben ne, bayan ya yi nasara a 14 cikin kananan hukumomi 22 na jihar, duk da kasancewar gwmanan jihar, Nasir El-Rufai, dan a-mutun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa ta APC, Bola Tinubu.

Baturen zaben, Farfesa Muhammad Zayyan Umar, ya sanar da cewa Atiku ya yi nasara da kuri’u 554,360.

Bola Tinubu na APC ya zo na biyu da kuri’u 399,293.

Jam’iyyar LP ta zo a matsayi na da kuri’u 294,494, sai  NNPP da ta samu kuriu 92,962.

Jam’iyyar LP ta lashe kananan hukumomi bakwai a yayin da APC mai mulkin jihar ta ci kananan hukumomi biyu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here