Jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, ta nesanta kanta daga kiraye-kirayen a soke zaben shugaban kasa na 2023 tare da kada kuri’ar rashin amincewa da shugaban INEC, daga jam’iyyar Labour da People’s Democratic Party.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugabar kwamitin amintattu, Sanata Misis Patricia Akwashiki, ta fitar a Abuja ranar Talata.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “ Hankalina ya karkata ga wata sanarwar manema labarai da shugaban jam’iyyar Labour ta kasa Julius Abure ya fitar a madadin jam’iyyar Labour Party, Peoples Democratic Party.
“Sun bukaci shugaban INEC ya sauka daga mukaminsa kuma a sake gudanar da sabon zabe. Wannan ba shine matsayin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ba. Ralph Nwosu wanda shi tsohon shugaban jam’iyyar ADC don haka ba shi da hurumin ya yi magana a madadin da ADC kuma ba zai iya magana da yawun ADC ba.