Kuri’ar da Al-mustapha ya samu a zaben shugaban kasa

0
106

Hamza Al-Mustapha, tsohon dogarin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha, ya zo na kusa da karshe a zaben shugaban kasa na 2023, wanda Bola Tinubu na jam’iyyar APC ya lashe.

Al-Mustapha, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a Jam’iyyar AA ya samu kuri’a 14,522, a zaben shugaban kasan da ’yan Najeriya miliyan 24.9 suka kada kuri’a.

Hasali ma, kuri’un da ya samu a zaben bai fi kashi daya da rabi cikin 100 da lalatattun kuri’un da aka jefa a zaben ba, wanda jam’iyyu 18 suka fafata a ciki.

Da yake sanar da sakamakon zaben, Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yaklubu, ya ce an jefa lalatattun kuri’a 939,278 aka jefa a zaban na shugaban kasa.

Daga Al-Mustapha sai wanda ya zo na karshe a zaben, Osita Charles da ya samu kuri’u 12,839.

Dan gwagwarmaya kuma mai kafar labaran intanet ta Sahara Reporters, Omoyele Sowore, na Jam’iyyar AAC, ya haura Al-Musta da kuri’a 86, inda aka jefa masa kuri’a 14,608 a zaben.

Duk da haka, jimillar kuri’un da shi da Al-Mustpha suka samu bai fi kashi cikin 100 na lalatattun kuri’ar da aka jefa a zaben ba.

Al-Mustapha mutum ne mai farin jini, kuma ba jimawa bayan fitowarsa daga gidan yari ya fara yin tsokaci a kan al’amuran da suka shafi Najeriya.

Jama’a da dama na ganin sa a matsayin daya daga cikin wadanda suka san matsalolin Najeriya ciki da bai, da kuma hanyoyin da za a magance su.

Si dai kuma tun da yake fitowa takara, bai taka fitowa a daya daga cikin manyan jam’iyyun Najeriya ba.

Haka shi ma Sowore, wanda jam’iyyarsa ta AAC karama ce, kuma mutane da tama na kallon sa a matsayin mai babatu, amma babu wani tasiri da yake yi a zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here