Buhari zai kaddamar da aikin wutar lantarki mai amfani da gas da kuma jajen gobarar kasuwar Borno

0
96

A yau Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci Maiduguri, babban birnin jihar Borno domin kaddamar da sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai amfani da iskar gas ta Maiduguri mai karfin megawat 50.

Tashar lantarkin wacce kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya gina, za ta samar da wutar lantarki megawatt 50 ga birnin Maiduguri da kewayen garin.

Babban birnin jihar ya fuskanci kalubalen rashin wutar lantarki irin wacce ba a taba ganin irinta ba a yankin sakamakon lalata tasoshin samar da wutar lantarkin da ‘yan ta’addar Boko Haram suka yi, sama da shekara daya.

Daga bisani kuma, shugaban a yayin ziyarar zai gana da jajantawa wadanda bala’in gobarar Kasuwar Monday ta Maiduguri ta shafa.

A ranar Lahadin da ta gabata ne wata gobara ta tashi a kasuwar Monday a Maiduguri, inda ta kone kasuwar baki daya. Gobarar ta lalata shaguna da kayayyaki na biliyoyin Naira.

Haka kuma zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi, kamar titin unguwar Bolori Layout, titin Ahmadu Bello Way, da dai sauransu yayin ziyarar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here