Dubun wani dan damfara da ke sojan gona a matsayin jamiāin Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) yana karbar kudin mutane ta cika a Jihar Kano.
Hukumar ta kama wanda ake zargin ne a Karamar Hukumar Wudil, inda yake amfani da sunanta yana karbar kudaden mutane da sunan zai tabbatar da sunayensu da bayanan gidaje ba su samu matsala ba a aikin kidayar mutane da gidaje da hukumar za ta yi nan ba da jimawa ba.
Mai magana da yawun hukumar, Jamila Abdulkadir, ta shaida wa āyan jarida cewa āWannan hukuma ta nesanta kanta da bayanan da ke yawo na karbar N5,000 don tabbatar da sunan wanda suka cike aikin kidaya na wucin-gadi a Jihar Kano.
āMun yi nasarar damke wani daga cikin masu yin wannan aika-aika a Karamar Hukumar Wudil tare da damka shi ga āyan sanda don gudanar da bincike.
āDa wannan ne hukumar take kara jan hankalin alāumma cewa su guji duk wasu da ke karbar kudi don tabbatar da bayanansu kan batun kidaya a Jihar Kano.ā
Ta kara da cewar, bisa bayanan da ta samu, ta sa jamiāan tsaro bincikar lamarin.