Gwamnatin Jihar Katsina ta sake jaddada kudurinta na tallafa wa ‘yan sanda wajen tabbatar da doka da oda gudanar da manyan zabuka masu zuwa a jihar.
Gwamna Aminu Bello Masari shi ya ba da wannan tabbacin a lokacin da amsar bakuncin sabon mataimakin babban sufeton ‘yan sanda mai kula da shiyya 14, da aka tura wanda suka kunshi jihohin Katsina da Kaduna da suka ziyarce shi.
Masari ya jaddada cewa gwamnatin jihar za ta yi duk abin da ya kamata domin kare al’ummar ta daga duk wata barazana. Sai dai ya ce jihar Katsina na bukatar karin jami’an ‘yan sanda domin samar da tsaro yadda ya kamata. Daga nan sai ya yi wa mataimakin babban sufeton ‘yan sanda fatan samun nasara wajen gudanar da sabon aikin sa.
Tun da farko, mataimakin babban sufeton ‘yan sanda, Ahmed Abdurahman ya ce ya je gidan gwamnati ne musamman domin sanar da gwamnan jihar cewa an turo shi ne domin sa ido wajen gudanar da babban zaben 2023.
Abdurahman wanda aka turo daga kwalejin horas da ‘yan sanda da ke Wudil a jahar Kano, ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar ya yi masa bayani a kan shirye-shiryen tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Ya ce haka kuma zai ke yi wa shiyoyin domin tabbatar da cewa an tanadi duk abin da ake bukata.
Kwamishinan ‘yan sanda, CP Kolo Yusuf wanda tuni ya kama aiki da kuma fara shirye-shiryen daukar matakai na samar da tsaro.
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Gambo Isa ya fitar.
Sanarwar ta gargadi masu karya doka da suka hada da ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka ko dai su bar jihar ko kuma a damke su tare da hukunta su daidai yadda doka ta tanada.
A kan haka ne, rundunar ke kira ga al’ummar jahar da su ci gaba da bayar da goyon baya da hadin kai ga ‘yan sanda don tabbatar da samun cikakkiyar nasarar gudanar da zabukan shekarar 2023 cikin kwanciyar hankali da lumana.