Shekarau ya ki karbar takardar shaidar cin zaben sanata

1
289

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya kaurace wa taron mika wa  zababbun Sanatoci takardar shaidar lashe zaben da aka gudanar.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Shekarau a matsayin wanda ya ci zaben Sanatan Kano ta Tsakiya da aka yi ranar 25 ga Fabrairu, 2023 a karkashin jam’iyyar NNPP.

Sai dai dan majalisar mai ci bai halarci taron mika takardar shaidar lashe zabe ga zababbun Sanatocin ba a ranar Talata.

Mai magana da yawun Malam Shekarau, Sule Y. Sule, ya shaida wa manema labarai cewa ya riga ya sanar cewa ba zai karbi kujerar Sanatan ba.

“Mun riga mun bayyana matsayinmu kan lamarin. Sanata Shekarau ba shi da sha’awa kuma ba zai karbi takardar shaidar lashe zaben ba,” in ji shi.

Bayan bayyana Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Kano ta Tsakiya, Shugaban Jam’iyyar NNPP na Kasa, Farfesa Rufa’i Alkali, ya ce Shekarau ya fice daga jam’iyyarsu amma abin takaici sai INEC ta ayyana shi a matsayin zababben Sanatan Kano ta Tsakiya a maimakon sunan Rufai Hanga.

Tun da fari an shiga rudani bayan da INEC ta sanar da Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben.

Amma jam’iyyar NNPP ta bayyana cewar ta aike wa da INEC a rubuce cewar Shekarau ya fice saga jam’iyyar.

Shi ma da kansa tsohon gwamnan na Kano, ya ce ya sanar da INEC a hukumance game ficewarsa daga jam’iyyar ta NNPP.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here