ECOWAS za ta karrama Buhari da lambar yabo

0
84

Yayin da ya rage saura kwanaki 83 shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki, zai samu lambar yabo ta dimokuradiyya da kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka za ta ba shi.

Shugaban kungiyar na yankin kuma shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Embalo ne, ya bayyana hakan a taron kasashen biyu da suka yi da Buhari a taron majalisar dinkin duniya kan kasashen da suka fi ci gaba a birnin Doha na kasar Qatar.

“Buhari zai sanya sunansa a cikin jerin sunayen karramawa a sabon ginin hedikwatar al’umma da aka kammala a Abuja,” wata sanarwa da babban mai taimaka wa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya sanyawa hannu a ranar Talata.

Sanarwar mai taken ‘ECOWAS ta bai wa shugaba Buhari lambar yabo ta dimokradiyya.

Embalo ya yi nuni da cewa, wannan karramawar ta amince da nasarorin da Buhari ya samu a fannin tsaro da inganta dimokuradiyya a matsayin tsarin gwamnati a fadin nahiyar.

A cewarsa, shugaban na Nijeriya ya yi aiki fiye da kowa wajen tallafawa gwamnatocin dimokuradiyya a yammacin Afirka, kamar yadda ya yi a yakin da ake yi da bullowar gwamnatocin da ba na dimokuradiyya ba.

“Don haka, in ji Shugaban ECOWAS, Shugaba Buhari zai sanya sunansa a cikin sabon ginin hedikwatar al’umma bayan an kammala shi a Abuja, domin al’ummar Afirka ta Yamma masu zuwa su san irin daukakar da ya samu kuma su kwaikwaya.”

Da yake mayar da martani, shugaban ya yi maraba da shawarar, inda ya jaddada cewa, dimokuradiyya wani abin dogaro ne wajen samun ci gaban kasa, domin ta hada kan mutane da al’adu daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here