Ba mu yi umarnin ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira ba – CBN

2
253

Babban bankin Najeriya CBN ya ce har yanzu bai baiwa bankunan kasuwancin kasar sabon umarni ba, bayan hukuncin da kotun kolin kasar ta yi kan ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin kasar da aka sauyawa fasali zuwa ranar 31 ga watan Disamba.

A lokacin wata ganawa da jaridar Daily Trust ta yi da mai magana da yawun bankin Isa Abdulmumin, ya ce babu wani umarnin da bankin ya baiwa bankunan kasar su rinka baiwa abokan huldar su tsofaffin kudin.

Amma wani babban jami’in bankin ya tabbatarwa da jaridar ta Daily Trust cewa tsofaffi da sabbin kudin nairan na da amincewar doka, don haka bai kyautu mutane su rinka kin amsar kudin ba.

Idan ba’a manta ba, a ranar Juma’ar da ta gabata ne alkalan kotun kolin Najeriya 7 karkashin jagorancin Inyang Okoro, su ka bayyana cewar umarnin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya baiwa babban bankin CBN na sauya fasalin naira dari 2 da dari 5 da kuma dubu daya ba tare da tun-tubar gwamnonatocin jahohi da sauran masu ruwa da tsaki ba sabawa doka ne.

Toh sai dai bayan hukuncin na ranar Juma’a, da dama daga cikin bankunan kasuwanci a kasar sun fara sanya tsofaffin takardun kudin naira da aka sauyawa fasali a na’urar cire kudi da kuma baiwa abokan huldar su a cikin bankuna.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here