Kotu ta tsare matasa biyu kan yi wa mai cikin wata 8 fyade a Abuja

0
193

Wata kotu da ke zamanta a yankin Gwagwalada a Abuja, ta tsare wasu makiyaya biyu da suka amsa laifin yin garkuwa da wata mata tare da yi mata fyade a gidan yari har zuwa ranar 22 ga watan Maris.

Mai gabatar da kara, Dabo Yakubu, ya shaida wa kotun cewa a ranar 25 ga watan Fabrairu, wadanda ake zargi, sun yi garkuwa da wata mata mai cikin wata takwas a gidanta da ke Karamar Hukumar Abaji.

Ya bayyana wa alkali cewa wadanda ake zargin sun kuma yi wa matar fyade a cikin dajin, ba tare da la’akari da cewa tan dauke da tsohon ciki ba.

Ya ce wani Abubakar Wakili a Karamar Hukumar Abaji ne, ya kai rahoton lamarin ofishin ’yan sandan yankin Gwagwalada a ranar 26 ga Fabrairu.

Mai gabatar da karar, ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 96, 262, 264, 387 na kundin laifuffuka.

Alkalin kotun, Malam Abdullahi Abdulkarim, ya dage yanke hukuncin ne domin ganin halin da mai juna biyun za ta tsinci kanta a ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here