Koriya ta Arewa: Kin Jung-Un ya umurci dakarun sa su yi damarar yaki

0
106

Shugaba Kim Jong Un ya umurci rundunar sojin  Korea ta Arewa  ta kara azama wajen shirin abin da ya kira ‘ainihin yaki’, bayan da shi da ‘yarsa suka sa ido a wani atisayen sojn kasar, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka ruwaito a wannan Juma’a.

Hotuna sun nuno Kim da ‘yarsa duk sanye da bakaken riguna, tare da  rakiyar wasu jami’an tsaro da ba sa sanye da kayan sarki, a yayin da suke kallon yadda sojin kasar ke atisayen harba makamai masu cin dogon zango a ranar Alhamis.

Tun da farko rundunar sojin Korea ta Kudu ta ce ta gano  cewa an harba wani makami mai cin dogon zango, kuma tana nazari a kan yiwuwar harba Karin makamai irin sa daga kusurwa guda.

A yayin da yake duba atisayen sojin, Kim ya shaida wa dakarun kasar cewa su kasance a shirye saboda wasu ayyuka biyu masu mahimmanci da zummar kare duk wani abin da zai haddasa yaki, ko kuma dauka mataki idan ya tashi.

Wannan atisayen na zuwa ne a daidai lokacin da  Koriya ta Kudu da Amurka ke shirin kaddamar da atisaye mafi girma a tsakaninsu a cikin shekaru 5 a ranar Litinin mai zuwa.

Dangantaka tsakanin Koriyoyin biyu na cikin yanayi mafi muni a cikin gwamman shekaru, inda Koriya ta Arewa ke ci gaba da gwajin haramtattun makamai, a yayin da Koriya ta Kudu  ke karfafa dangantaka da Amurka.

Wannan ne atisaye mafi girma na Koriya ta Arewa da diyar Kim, wanda ake kira Ju Ae ta halarta. Da dama na daukar ta a matsayin wadda za ta gaji Kim.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here