Babbar Kotu a Abuja ta daure wata ’yar kasuwa tare da kamfaninta mai suna T.M Properties Limited, shekara 24 a kurkuku saboda karbar kudi Dala 298,000 daga kamfanin Bacab Properties Limited ta hanyar damfara.
Kazalika, mai laifin ta karbi kudi Naira miliyan 40 da sunan ita ce mai wani fili mai lamba 1721 da ke yankin Jahi a Abuja.
Aminiya ta rawaito Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta gurfanar da matar a ranar 20 ga Oktoba, 2021 inda ake tuhumar ta da laifuka hudu.
Sai dai ta ki amsa tuhumar da suka hada da karbar kudade ta hanyar karya da amfani da takardu da bayanan bogi.
Da take yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a E. Okpe, ta ce mai tuhuma ya gabatar wa kotun gamsassun bayanai da hujjoji a kan mai kare kanta.
Da yake ba da bayani, mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce hukunce-hukuncen za su gudana ne lokaci guda.
Ya kara da cewa, kotun ta bukaci mai laifin ta maida kudade Dala 298,000 da Naira miliyan 41 ga mai kara.
Ya ce yayin shari’ar, wadda aka fara tun ran 1 ga Fabrairu, 2022, mai gabatar da kara ya gabatar wa kotu shaidu guda shida da takardu 14 a matsayin hujjoji.
“Yayin da masu kare kai suka fara kare kansu ran 1 ga Nuwamba, 2022, inda mai kare kai ta farko ta ba da shaida a kan kanta da kuma a madadin mai kare kai na biyu,” in ji Uwujaren.
Ya ce bayan da kotun ta saurari duka bangarori a wancan lokaci, daga nan ta dage shari’ar zuwa 7 ga Maris, 2023 domin yanke hukunci.