An gaza binne gawar tsohon shugaban majalisar dattawa saboda rashin kudi

0
79

An rasa yadda za a yi da gawar marigayi Sanata Joseph Wayas, Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya a jamhuriyya ta biyu, a wani asibiti da ke Landan.

Wayas dai kamar yadda wakilinmu ya ruwaito, ya rasu ne tun a watan Disambar 2021, a wani asibiti da ke Landan sakamakon jinya ta tsawon lokaci da ya yi fama da ita.

Sanata Wayas wanda ya jagoranci Majalisar Dattawan Najeriya a tsakanin shekarar 1979 zuwa 1983, iyalansa sun alakanta talauci da rashin lafiyarsa da ta ki ci ta cinye wa.

Makusantan nasa dai sun shaida wa Aminiya cewa, taimakon kudi da ke shigo musu ne ya yanke, lamarin da ya sanya suka gaza dawo da gawarsa gida Najeriya har a iya binne ta.

Tun a watan Disambar bara ne dai Gwamna Ben Ayade na Jihar Kuros Riba, inda marigayin ya fito, ya kaddamar da wani kwamiti da zai jibinci lamarin jana’izar tsohon Shugaban Majalisar Dattawan.

Wannan dai ya biyo bayan umarnin da gwamnatin jihar ta bai wa Kwamishiniyar Lafiya ta lokacin, Dokta Betta Edu da ta kula da harkokin lafiyar marigayin a Landan.

Rahotanni sun ce gwamnatin jihar ta fitar da wasu kudade ga kwamitin jana’izar karkashin jagorancin tsohon Atoni-Janar kuma Ministan Shari’a, Kanu Agabi.

Sai dai bayan watanni 14 da rasuwarsa, bincike ya nuna cewa an yi watsi da gawar tsohon Shugaban Majalisar Dattawan duk a kan takaddamar kudade.

Haka zalika, bincike ya nuna cewa takaddamar kudaden jana’izar ce ta sanya wasu manyan mambobin kwamitin suka yi murabus.

Daya daga cikin manyan ’yan kwamitin wanda ke zaman tsohon Babban Sakataren Hukumar Tsare-Tsare ta Kasa, Ntufam Fidelis Ugbo, ya tabbatar da cewa tun a wancan lokaci ya fice daga kwamitin amma bai bayyana dalilansa ba.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnan ya bayar da kudade domin jana’izar, amma ya ce babban dan marigayin, Mista Joseph Wayas jr, shi ya fi cancantar bayyana dalilin da ya sa har ya zuwa yanzu ba a binne gawar mahaifinsa ba.

“Ba zai yiwu a ce ba shi da wani bayani da zai bayar game da dalilin da ya sa aka jinkirta jana’izar ba.

Shi ne dan fari. Ya kamata ya kasance mai kula da…”, Ugbo ya shaida wakilinmu cikin mamaki.

A zantawar Mista Wayas Jr. da Aminiya, ya bayyana cewa kwamitin jana’izar ke da alhakin gudanar da jana’izar, saboda haka ba shi da wani abin cewa a kai.

Ya yaba wa Gwamna Ayade bisa goyon bayan da ya bai wa kwamitin, sai dai ya bayyana takaici yadda aka shafe watanni 14 amma gagara binne gawar mahaifinsa.

“Jana’izar ba a hannunmu take ba, amma a hannun kwamitin da Gwamna Ayade ya dora wa nauyi.

“Na ji akwai batutuwan da suka shafi kudaden da aka fitar saboda jana’izar. Kuma an ce wasu mambobin sun yi murabus.

“Ba zan iya koma wa gwamnan ba a yanzu saboda batun zabe. Saboda ya riga ya yi nasa kokarin.”

A wata hira da aka yi da shi a baya, Mista Wayas Jr ya yi nadamar jinkirin da aka samu wajen gudanar da jana’izar mahaifinsa, amma ya roki a mutunta gawar nan ba da dadewa ba.

Wayas Jr ya yi godiya ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda ya dauki nauyin tafiyar mahaifinsa zuwa Landan lokacin da ya fara jinya.

Ya ce mahaifinsa ya samu mafi kyawun kulawar jinya, amma gudunmawar da ya bayar ta kare cikin watanni uku.

A cewarsa, kafin rasuwar mahaifinsu, ‘yar uwarsa ce a Landan ta ci gaba da dauki nauyin jinyarsa, kuma ta ci gaba da daukar nauyin ajiyar gawar tun shekarar 2021.

Da yake tsokaci, Babban Sakatare a Ma’aikatar Lafiya ta jihar, Dokta Iwara Iwara, ya ce, “Kamar yadda aka sani, gwamnan jihar ya kaddamar da wani kwamiti. Amma tun daga wannan lokaci ban kara jin wani abu a kai ba.

“Saboda haka a yanzu ba zan iya ba da dalilan da suka sa aka jinkirta jana’izar ba.”

Babban mashawarcin gwamnan kan harkokin yada labarai, Barista Christian Ita, ya ce, “Ba na son shiga cikin lamarin.

“Watakila babban dan marigayin ne matsalar. Amma a tuntubi mambobin kwamitin jana’izar don a gaskiya gwamnan ya fitar da kudin jana’izar tun da dadewa.”

Aminiya ta kuma nemi jin ta bakin Kwamishinan Labarai na jihar, Eric Anderson, amma dai bai amsa kiran da aka yi masa ba da kuma sakon kar ta kwana da aka tura masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here