Sama da ‘yan Najeriya miliyan 10 sun yi ta’ammali da tabar wiwi a shekarar bara

0
77

Hukumar Kula da Inganci Abinci da Magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta ce mutane miliyan 10 da dubu dari 6 ne suka yi amfani da tabar wiwi a shekarar da ta gabata, adadin da yake wakiltar kaso 10.8 na al’ummar kasar.

Ta ce, rahoton ya bayyana cewa tabar wiwi ce kwayar da aka fi amfani da ita, inda matsakaicin shekarun masu amfani da ita a cikin al’umma 19 ne.

Shugabar ta NAFDAC ta ce Najeriya ba za ta goyi bayan halasta amfani da tabar wiwi ba, duba da cewa ba ta da isassun kudaden da za ta yaki nomarta ba bisa ka’ida  ba da kuma wuce makadi da rawa wajen amfani da ita.

Ta ce hakkin tabbatar da an yi amfani da tabar wiwi don samar da waraka ya rataya ne a wuyar hukumarta idan har aka halasta ta, kuma za ta yyi wanna aiki ne tare da tabbatar da ba a karkata ta zuwa harkar shaye shaye don maye ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here