Kotu ta daure odita-janar na Yobe shekaru 5

0
273

Alhaji Idris Yahaya, odita janar na kananan hukumomin jihar Yobe, zai yi zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar, bayan da Mai Shari’a Muhammad Lawu Lawan na Babbar Kotun Jihar Yobe ya yanke masa hukunci.

Kotun ta yanke wa Yahaya hukuncin ne a lokacin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da shi a ranar Litinin.

An yanke masa hukuncin ne bayan da aka same shi da laifin almundahanar Naira miliyan 19 da hukumar EFCC shiyyar Maiduguri ta bankado.

Rahotanni sun bayyana cewa Yahaya ya karbi kudade daga ofishin babban mai binciken kudi na kananan hukumomi da masarautu na jihar Yobe domin siyan mota kirar Toyota Corolla ta shekarar 2015, sannan ya karkatar da wani bangare na kudin domin amfanin kansa.

Mai laifin wanda aka fara gurfanar da shi a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba, 2022, ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

A ci gaba da shari’ar, lauyan EFCC, Mukhtar Ali Ahmed, ya kira shaidu hudu da kuma takardun bayar da shaida wadanda aka shigar da su.

Da yake yanke hukunci a ranar Litinin, Mai shari’a Lawan ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhumar da ake yi wa wanda ake tuhuma tare da yanke masa hukunci kamar yadda ake tuhuma.

Don haka ya yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari tare da zabin tara.

Alkalin ya kuma umarci wanda ake tuhuma da ya biya kudin diyya 100,000.00 ga gwamnatin jihar Yobe ta hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ko kuma ya kara shekaru biyu a gidan yari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here