An yi yunkurin yiwa INEC kutse sau fiye da miliyan 12- Gwamnati

0
158

Gwamnatin Najeriya ta ce sau miliyan 12 da dubu 988 da 978 aka yi yunkurin yin kutsen sata ko sauya bayanan sakamakon zaben shugabancin kasar da ya gudana a ranar 25 ga  watan Fabarairun da ya gabata.

Ministan ma’aikatar sadarwar zamani da tattallin arziki na Najeriya Dakta Isa Ali Pantami, ya ce da farko an rika kai harin na yi wa muhimman shafukan gwamnati kutse ne akalla sau  miliyan 1 da dubu 55o a kullum kafin ranar zaben na shugaban kasa.

Sai dai a ranar zaben wato 25 ga watan Fabarairu an ga karuwar kai makamantan hare-haren da kutsen zuwa miliyan 6 da dubu  997 da dubu 277 a rana guda, wadanda aka kai daga  ciki da wajen Najeriya.

Wasu dai na alakanta fuskantar yunkurin kusten da daya daga cikin dalilan da suka sanya hukumar zaben Najeriya INEC kin sanya bayanan sakamakon zaben da aka yi  a rumbunta na yanar gizo kamar yadda aka zaci za ta yi a baya, matakin da bai yi wa jam’iyyun adawa da dama dadi ba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here