Kotu ta daure tsohon kwamishina shekara 3 a Imo

0
59

Wata babbar kotun jiha da ke zamanta a Owerri, babban birnin jihar Imo, ta yanke wa tsohon kwamishinan sufuri a karkashin gwamnatin Rochas Okorocha, Laz Okoroafor-Anyanwu, hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari, bayan da aka same shi da laifukan da suka shafi zamba da sata.

Da ta ke yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai shari’a K.A Lewanya, ya ce Okoroafor-Anyanwu an same shi da laifin karkatar da Naira miliyan 180 na kudaden jihar zuwa asusun wani kamfani mai zaman kansa.

Alkalin ta ce ya kasance babban mai hannun jari a kamfanin.

A cewar mai shari’a, Okoroafor-Anyanwu an kuma same shi da laifin karya dokar siyan kaya, cin zarafin ofis, da kuma yin amfani da ofishinsa wajen samun tagomashi da bai dace ba a cikin harkokinsa a lokacin da yake rike da mukamin kwamishina.

Ya ce lauyan Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Barista Michael Ani, wanda shi ne lauyan mai shigar da kara ya tabbatar da babu shakka cewa lokacin da Okoroafor-Anyanwu yake kwamishinan a tsakanin 2015 zuwa 2019, ya mika zunzurutun kudi har Naira miliyan 100 daga asusun ITC zuwa kamfanin mai zaman kansa mai suna Oma Oil Industries Limited wanda ya sabawa sashe na 12 da 19 na dokar ICPC ta 2020 na ma’aikacin gwamnati.

Alkalin kotun ta kara da cewa, a irin wannan hali, Okoroafor-Anyanwu ya sanya hannu a kan wasu kudi har Naira miliyan 80 daga asusun gwamnati kai tsaye zuwa asusun kamfaninsa mai zaman kansa kan cewa zai sayo wasu motoci don gudanar da ayyuka ba tare da bin ka’ida da bin doka da oda na ma’aikatan gwamnati ba.

Ko da yake Okoroafor-Anyanwu ya ki amsa laifinsa, alkalin da ta yanke hukuncin daurin shekara daya a gidan yari ba tare da zabin tara ba.

Alkalin ta kuma yanke hukuncin cewa kudin da aka wawure Naira miliyan 180 da aka samu a asusunsa, a mika su ga Kamfanin Sufuri na Jihar Imo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here