FCTA ta rushe fitacciyar unguwar Durumi ‘Monkey village’ da ke Abuja

0
104

Hukumar dake kula da babban birnin tarayya Abuja FCTA, ta rusa wani fitaccen jerin gidaje da ke unguwar Durumi da aka fi sani da ‘Monkey village’ a cikin babban birnin Abuja.

FCTA ta bayyana kauyen a matsayin wani yanki da ya zama maboyar miyagun mutane bayan sun aikata munanan ayyuka a kan mazauna yankin.

Daraktan hukumar tsaro na babban birnin tarayya Abuja, Adamu Gwary, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a yayin rusau din, ya koka da yadda al’ummar kauyen ke tafka ta’asa.

 

Daraktan sashen kula da ci gaban birnin, Mukhtar Galadima, ya ce, wannan aiki na daya daga cikin aikin tsaftar birnin Abuja wanda ministan babban birnin tarayya, Malam Muhammad Bello ya bayar da umurni a watannin baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here