Alakar sauya kwamishinan ’yan sanda sau 5 a Kano da zabe

0
90

Sau biyar cikin dan kankanin lokaci rundunar ’yan Sandan Najeriya ta nada tare da sauya kwamishinan ’Yan Sanda da ta tura Jihar Kano.

Wannan dambarwa na da nasaba da Siyasar Kano gabanin zaben gwamnoni da ’yan majalisar dokokin jiha da za a gudanar ranar Asabar, 18 ga watan Maris da muke ciki.

Idan za a a iya tunawa a baya, Jam’iyyar APC mai mulkin jihar da kuma manyan jam’iyyun adawarta a jihar, irin su NNPP da PDP sun zargi wasu daga cikin Kwamishinonin ’Yan Sandan da aka sauya da shiga harkokin siyasar jihar.

ِAna iya tunawa cewa a ranar 21 ga watan Farbariru, 2022, Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, ya dauke Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Mamman Dauda, zuwa Jihar Filato.

Shi ma Muhammad Yakubu ba a dade ba aka sauya masa wurin aiki, aka maye gurbinsa da  Balarabe Sule a mastayin sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano.

Sai dai ba a je ko’ina ba, shi ma a ranar 8 ga watan Maris, aka sauya shi, bayan korafin cewa shi din tsohon Babban Jami’in Tsaro (CSO) na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Bayan nan ne aka tura Faleye Olaleye a matsayin sabon kwamishina, amma ba a kai ko’ina ba, aka janye shi, aka maye gurbin sunansa da Ahmed Kontagora a matsayin wanda zai jagoranci rundunar a lokacin zaben da ke tafe.

A ranar Talata kuma aka sauya shi Kontagora, aka kawo Usaini Gumel a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Shin Kano ne kadai?

Sai dai Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda mai kula da zaben shiyyar Arewa maso Yamma, Hafiz Inuwa, ya bayyana cewa sauye-sauyen kwamishinonin ’yan sandan da aka gani ba abu ne da ya kebanci Jihar Kano ba.

Inuwa, wanda ya je Kano a shirye-shiryen zaben ya ce, “An yi sauye-sauyen Kwamishinonin ’Yan Sandan ne domin tabbatar da ganin ’yan sanda ba su tsoma baki a harkokin siyasa ba; manufar ita ce yin ba-zata.”

Ya kara da cewa sauya musu wurin aiki wani shiri da zai tabbatar “cewa babu wani mahaluki da zai ja akalar ’yan sanda kan yadda za su gudanar da aikinsu.

“Manufar Shugaban ’Yan Sandan Najeriya ita ce tabbatar da aminci da kuma zabe mai inganci da samun karbuwa ga al’umma; Wannan shi ne dalilin sauye-sauyen da aka gani a baya-bayan nan.”

Ya shaida wa ’yan jarida cewa yana tattaunawa da malaman addini da kuma ’yan siyasa da jam’iyyu a Jihar Kano, su tabbata sun gargadi yaransu kada su kuskura su tayar da hankali ta hanyar duk wani furuci ko aiki, domin kuwa duk wanda ya fada komar ’yan sanda ba zai ji da dadi ba.

A cewarsa, “Mun shirya yin maganin duk wani bata-gari, musamman a Kano, da ma sauran sassan kasar nan.

“Shugaban Kasa da kuma Shugbana ’Yan Sanda sun umarce mu… cewa duk wanda ya nemi kawo tarnaki a harkar zabe, to duk abin da ya zame shi ya kuka da kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here