An kashe mutum 4 a rikicin jami’an tsaro da ’yan Shi’a a Kaduna

0
116

An kashe mutum hudu a wani rikici tsakanin mabiya akidar Shi’a da jami’an tsaron Gwmana Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna.

An yi artabun ne a lokacin da El-Rufai ya kai ziyara a unguwar Bakin Ruwa a ranar Alhamis da yamma.

Jami’an tsaron sun bude wuta ne bayan wasu mabiya Shi’a sun fara jifar ayarin gwamnan a yayin ziyarar.

Lamarin dai ya jefa al’ummar yankin cikin tashin hankali, a yayin da shaidu suka tabbatar da rasuwar mutum hudu sakamakon arangamar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here