Rikici ya barke a mazabar Abba gida-gida da Abdullahi Abbas a Kano

0
180

A maimakon a fara zabe kamar yadda aka tanada, rikici ya mamaye wani yanki na Unguwar Chiranci da ke zaman mazabar dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida da kuma Shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas.

Cikin wani hoton bidiyo da wakilinmu ya nada, jami’an ’yan sanda rike da bindigogi ke ta kai kawo a tsakanin jama’a da ke nuna alamar tsugune ba ta kare ba.

Unguwar Chiranci wadda ke cikin Karamar Hukumar Gwale, tana da tarin rumfunan zabe, inda kuma tun ba yanzu ba an yi hasashen babu lallai a kwashe lafiya saboda tsananin adawa ta siyasa da ke tsakanin jam’iyyar NNPP da kuma APC mai mulki a jihar.

Bayanai dai sun ce ’yar tazara kalilan ce tsakanin rumfunan zabe da jiga-jiga jam’iyyun mabambanta za su kada kuri’arsu.

Daga bisani dai kura ta lafa a kuma an kammala shirin soma aiki zabe a mazabar da ke Sakandaren GSS Balarabe Haladu a Unguwar ta Chiranci, inda ake sa ran nan da zuwa wani lokaci Abba Gida-Gida zai fito ya kada kuri’arsa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here