Abba gida-gida ya lashe zaben gwamnan Kano

0
92

Hukumar Zabe ta Kasa, INEC ta sanar da cewa jam’iyyar NNPP ta lashe zaben gwamnan Kano.

Dan takarar jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya zama wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano.

A sakamakon karshe da Baturen Zaben ya sanar: Farfesa Ahmad Doko Ibrahim, Abba Gida Gida ya samu kuri’a 1,019,602 yayin da dan takarar APC, Nasir Yusuf Gawuna da ya zo na biyu ya samu kuri’u – 890,705.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here