Asusun tallafawa yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce kimanin yara miliyan 78 suna fusantar hadarin kamuwa da cuttutukan da suke yaduwa ta ruwan sha guda uku.
Wannan bayyanin yana kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Babban Darektan shirin WASH na UNICEF Dr. Jane Bevan wacce aka fitar a yau Litinin.
“Kaso daya cikin uku na yara a Najeriyya ba sa samun tsaftattacen ruwan sha a gidajensu, kana, kaso biyu cikin uku na yara ba su da makewayi.
“Ba kasafai ake mai da hanakli wajen kula da tsaftar hannu ba inda kaso uku cikin hudu na yara kanan ba su da halin wanke hannayensu sakamakon rashin tsaftattacen ruwa da kuma sabulu a gidajensu.”
Bisa wannan dalili ne ya sanya Najeriya kasancewa daya daga cikin kasashe goma da suke fama da mutuwar yara a sakamakon cuttutukan da ake kamuwa da su a dalilin rashin wanke hannu kamar cututukan da suka danganci amai da gudawa, Bevan ta ce.
Ta kuma yi kira da a baiwa batun samar da tsaftattacen ruwan sha da zai dace da muhalli da bayyukan lafiyar jiki kulawa.
A cewarta, daukar wannan matakin ba kare lafiyar yaran kawai zai yi ba, amma zai taimaka wajen tbbatar da dorewar al’uma mai zuwa nan gaba.
Ta ce,“na tabbata muna bukatar inganta kulawar da muke bayarwa a wannan fanni ba tare da bata lokaci ba, har da samun kudade daga asusun muhalli ta duniya, ingantya hanyoyin kare muhalli a shirin WASH da al’ummomin da ake gudanar da shirin.
Ta kara da cewa “a inganta tasiri da hanyoyin bin dididgi da kwarewa domin samar da ayyukan ruwan da tsafta, sannan a kaddamar da kudurin majalisar Dinkin duniya ta SDG6 tare da la’akari da shirin inganta tsarin.