Majalisa za ta binciki musabbabin yawan hatsarin jirgin kasa a Najeriya

0
103

Majalisar Wakilai ta umarci kwamitin ta kan harkokin sufuri da ya binciki yawan hatsarin jiragen kasa da yake janyo asarar rayuka da dukiyoyi a fadin kasar nan.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Unyime Idem (PDP, Akwa Ibom) ya gabatar wanda ya bayyana cewa jerin haduran jiragen kasa sun yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi a Najeriya.

Ya ce, “A watan Janairun 2023, an samu rahoton wani hatsarin jirgin kasa a Kubwa da ke Abuja wanda ya yi sanadin mutuwar wata mata Selimota Suleiman, ma’aikaciyar gidan talabijin na NTA.

“A ranar Alhamis 9 ga watan Maris, 2023, wani jirgin kasa ya kutsa kai cikin wata motar safa ta BRT a Jihar Legas, inda ya yi sanadin mutuwar mutum shida tare da jikkata wasu da dama.

“A ranar 28 ga Maris, 2022, an kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna hari kuma ‘yan Najeriya da dama sun rasa rayukansu; yayin da wasu suka samu raunuka sannan aka sace wasu.

“Jirgin kasan Warri zuwa Itakpe ya kauce hanya a cikin dajin Kogi, inda akalla fasinjoji 300 suka makale cikin wata guda bayan an sace fasinjoji kusan 20 daga tashar jirgin kasa a Igueben a Jihar Edo”.

Ya ce duk da irin halin da ake ciki na rashin kulawar da wasu ke yi, ba taba dora alhakin faruwar hakan a kan wani ba.

Ya kara da cewa: “Wadannan al’amura marasa dadi sun faru sau da yawa saboda ba a dauki matakin hana faruwarsu a gaba ba.”

Don haka majalisar ta umarci a binciki musabbabin aukuwar haduran jiragen kasa daban-daban a fadin kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here