Na ji dadi wasu ‘yan takarar sun sha kayi – Buhari

0
160

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya sanar da cewa idan aka yi la’akari da yadda aka gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaben 2023 ba tare da yin wani katsalandan ba, ya nuna cewa ‘yan Nijeriya sun san wanda zai jagorance su.

Buhari wanda ya nuna gamsuwarsa kan yadda ‘yan Nijeriya suka yanke hukuncin wanda za su zaba a matsayin shugaban kasa da gwamna da ‘yan majalisar tarayya da na ‘yan majalisar jihohi, hakan ya nuna cewa, mulkin dimokuradiyya a kasar nan ya bunkasa.

Ya ce “Na ji dadi wasu ‘yan takarar sun sha kayi, na kuma ji dadi kan yadda masu jefa kuri’a suka yanke hukuncin kan wadanda suka zaba.

Buhari ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da hadiminsa na yada labarai Garba Shehu, ya fitar a ranar Talata, yayin da yake ganawar bankwana da Jakadiyar Amurka a Nijeriya, Mary Beth Leonard a Nijeriya, inda ya ce, ya gamsu da gudunmawar da ya taka kan tsarin zabe

Ya gode mata kan ayyukan ci gaba da ta bayar a kasar nan a lokacin zamanta musamman kan kara kulla huldar Difolomasiyya a tsakanin Nijeriya da Amurka.

A nata jawabin Jakadiyar ta ce, ta ji dadin nasarar da aka cimma wajen kara karfafa harkar Difolomasiyya a tsakanin Nijeriya da Amurka, musamman kan tsarin samar da biza ta shekaru biyar a tsakanin kasashen biyu da kuma hadar kasashen biyu kan harkar inganta tsaro da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here