Kungiyar masu rajin kafa ‘yantacciyar kasar Biafara ta IPOB, ta sha alwashin daukar mataki mai tsauri kan ‘yan kabilar Yarabawan da suka ci zarafin kabilar Igbo a jihar Lagos da ke Najeriya.
daukar matakin kan duk wani cin zarafi da aka yi wa ‘yan kabilar Igbo a jihar Lagos.
Kungiyar ta kuma gargadi ‘yan kabilar ta Igbo da su daina zuba jarin da ssuke yi a Legas din, tare da bukatar su da su koma yankunan su, inda IPOB ta kuma kara da cewa ya kamata ‘yan kabilar su fara kokarin kare kan su, ta hanyar kafa wata ‘yar karamar kungiya.
“Ra’ayin kyamar kabilar Igbo, barazana, hare-hare, da kuma yi wa ‘yan kasuwar Igbo sata, da barazanar da ake musu na su fice daga Legas, barazana ce ga daukacin kasar Biafra” in ji sanarwar.
“Abin takaici ne yadda shugabannin siyasa da na gargajiya na Yarabawa suka yi shuru kan yadda ake ci gaba da nuna kyama ga ‘yan kabilar Igbo a birnin Legas na Najeriya, wanda hakan ya nuna cewa suna kan hanya daya don fatattakar Ndigbo daga Legas.