Sama da ‘yan cirani 30 ne suka nutse a teku

0
189

Hukumomin Tunisia sun ce aƙalla ‘yan ciranin Afrika 34 ne suka nutse a cikin tekun birnin Sfax da ke Tunisia, ciki har da jarirai da ƙanan yara.

Karo na biyar kenan da aka fuskanci irin wannan kifewar jirgin a kwana biyu.

Rahotanni sun ce mutum 67 ne suka bata yayin haɗarin.

Jami’an Tunisia sun ce ana ƙara samun yawan jiragen ‘yan cirani a kullum da ke son tsallakawa Italiya.

Masu gadin iyakar ruwan sun ce sun dagakatar da sama da jiragen ruwa 50 cikin waɗannan kwanaki biyu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here